IQNA

Kungiyar EU Ta Ware Euro Miliyan 34 Domin Taimakon Mutanen  Gaza

22:38 - June 02, 2021
Lambar Labari: 3485975
Tehran (IQNA) Kungiyar tarayyar turai ta sanar da ware euro miliya 34 domin fara gudanar da ayyuka na taimaka ma al’ummarv yankin zirin Gaza.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, wakilin kungiyar tarayyar turai a Falastinu ya fadi a gaban wani taron manema labarai a birnin Ramallah cewa, dole ne Isra’ila ta kawo karshen killace yankin zirin Gaza da take yi, domin hakan yana cutar da daukacin al’ummar yankin.

Wakilin na tarayyar turai ya ce,a  shirye suke su bayar da dukkanin gudunmawar da ta kamata domin sake gina yankin zirin Gaza da kuma taimka ma al’ummar yankin, da ma sauran dukkanin yankunan Falastinawa.

Ya ce sake gian yankin zirin Gaza ba yana nufin sake gina gine-ginen da Isra’ila ta rusa a yankin ne ba kawai, baya ga haka sake gina zirin Gaza ya hada da kawo karshen killacewar da Isra’ila take yi wa yankin, tare da barin al’ummar yankin su ci gaba da kai komo da kuma harkokinsu na kasuwanci tare da sauran bangarori na duniya.

Baya ga haka kuma wakilin kungiyar tarayyar turan ya jaddada cewa, babu wani abu da zai halasta wa Isra’ila mamaye yankunan Falastinawa da majalisar dinkin duniya ta amince da iyakokinsu.

Daga karshe ya bayyana cewa, ware euro miliyan 34 da tarayyar turai ta yi domin fara taimaka ma al’ummar Gaza somin tabi ne na sauran ayyukan taimako da za su biyo baya.

3975089

 

captcha